A Benin ana fuskantar karancin mata wakilan al'umma a cikin hukumomin kasa, a masalan ce a kotun koli ta kasar mata 2 ne daga cikin mambobi 7, a yayin da ke da mata 6 cikin mambobi 83 na majalisar kasar, bangaren gwamnoni babu mace ko daya daga cikin gwamnoni 6 na jihohi, a karshe mata 8 ke da koye a cikin ministoci 26 na gwamnati ta yanzu ta shugaba Boni Yayi.
Cewar Pelagie Assogba, wannan rashin samun wakilci ga mata na da nasaba ne da abubuwa kamar rashin ilmin boko, abun da ke dabaibaye su a cikin al'umma kasar Benin ta fannin ci gaba. Kamar yadda alkaluman kididdiga na lisafin al'ummar kasar da aka gudana a watan Febrairu na shekara ta 2002 suka nuna, yawan mata ya kasance kishi 52 cikin 100 na al'ummar kasar ta Benin a cikin al'umma miliyan 8.(Abdou Halilou)