in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan kasashen duniya za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Ukraine
2014-02-20 20:47:34 cri
A yau alhamis 20 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, madam Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar na fatan kasashen duniya za su taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bangarori daban daban na Ukraine domin daidaita matsaloli ta hanyar yin shawarwari, da tabbatar da zaman lafiya a kasar cikin lokaci.

Rahotannin baya bayan nan na cewa ana ci gaba da zanga-zanga a Kive, babban birnin kasar Ukraine, inda zuwa jiya Laraba 19 ga wata, tashe-tashen hankula masu alaka da hakan suka janyo rusuwa, tare da jikkatar mutane dari takwas. Wannan dai lamari ya yi matukar janyo hankalin gamayyar kasa da kasa.

A ran 19 ga wata, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Ukraine ta bayyana cewa, mutane 26 ne suka rasu a sanadiyyar rikice-rikicen da suka auku a kasar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China