in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ukraine ya ziyarci gidan rediyon kasar Sin
2013-12-05 13:24:29 cri

Shugaban kasar Ukraine Viktor Fedorovych Yanukovych, wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin, ya kawo ziyara gidan rediyon CRI dake nan birnin Beijing na kasar Sin.

Shugaban Yanukovych, wanda ya shigo gidan Radion na CRI a safiyar Alhamis din nan 5 ga wata, ya kuma halarci bikin kaddamar da tashar rediyo ta yanar gizo a harshen kasar Ukraine, bikin da ya zo daidai da lokacin cika shekaru biyar da bude shafin yanar gizo CRI ONLINE da harshen kasar ta Ukraine.

An dai kaddamar da wannan shafi ne a shekarar 2008, wanda kuma a yanzu haka ya zama kafa daya kacal a nan kasar Sin, dake yada labaru da harshen kasar ta Ukraine. Ban da haka, wannan tashar rediyon ta shafin yanar gizo ita ce irinta ta 19, da gidan Radion CRI ya kafa, domin gabatawa masu sauraro tarihi, da harkokin al'adun al'umma, da tattalin arzikin kasar Sin da kuma yadda zaman rayuwar wasu jama'ar Ukraine suke a nan kasar Sin.

An ba da labarin cewa, yanzu haka shafin yanar gizon na CRI ONLINE, na gabatar da shirye-shirye ta amfani da harsuna 65, wanda hakan ya sanya shi kasancewa shafin yanar gizo dake amfani da harsuna mafiya yawa a duniya. Ya na kuma samun masu ziyara daga kasashe ko yankuna fiye da 160. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China