in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jari da Sin ta shigo da ta fitar dukkansu sun karu
2013-12-20 16:49:21 cri

Kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Shen Danyang, ya bayyana cewa tsakanin watan Jarairu zuwa Nuwambar bana, masu zuba jari na kasar Sin sun zuba jari kai tsaye ga kamfannonin ketare 4522 dake kasashe ko yankuna 156.

Mr. Shen ya kara fa cewa yawan kudin da Sin ta zuba ga kasashen waje, wanda da ba su shafi sashen hada-hadar kudi ba, ya kai dala biliyan 80.24, adadin da ya karu da kashi 28.3 bisa dari idan an kwatanta da na bara war haka.

Ya ce cikin wadannan watanni, yawan kudin da babban yankin Sin ya zubawa a wurare da kasashe mafiya ci gaba a fannin tattalin arziki ya kai fiye da dala biliyan 57.87, ciki hadda yankin Hongkong, da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashen Asiya ta ASEAN, da kungiyar kawancen kasashen Turai ta EU, da kasashen Austriliya, da Amurka, da Rasha, da Japan, adadin da ya kai kashi 72 cikin dari bisa na dukkan jarin da Sin ta zuba, ya kuma karu da kashi 19 cikin dari idan an kwatanta shi da na bara war haka.

Har ila yau kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar ta Sin ya bayyana cewa, yawan jarin da Sin ta yi amfani da shi a cikin wadannan watanni, yawan sabbin kamfanonin dake da jarin kasahen ketare ya kai 20434, adadin da ya ragu da kashi 9.19 cikin dari idan an kwatanta da na makamancin lokacin a bara, yawan jarin waje da Sin ta yi amfani da shi kuma ya kai fiye da dala biliyan 105, wanda ya karu da kashi 5.48 cikin 100 bisa na bara war haka, karuwar da ta auku a cikin watanni goma a jere.

Bugu da kari Shen Danyang ya kara da cewa, sashen ba da hidima ya taka rawar gani a fannin jarin ketare da aka zuba, inda yawan jari da kasashen dake nahiyar Asiya, EU da Amurka suka samar ya karu cikin sauri. Ban da haka, yawan jarin waje da ake amfani da su a yankin tsakiyar kasar Sin ya karu da sauri. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China