A cikin rahoton, an bayyana cewa, a cikin kasashe masu wadata, tattalin arzikin Amurka zai karu da kashi 2.5 cikin 100 a shekarar 2014, yayin da tattalin arziki na kasashen Turai ya samu kyautatuwa a shekarar 2013.
Rahoton ya ce, a yankunan kasashe masu tasowa, tattalin arzikin kasashen Afrika zai samu babban ci gaba, kuma an yi hasashe cewa, tattalin arzikin kasashen Afrika zai karu da kashi 4.7 cikin 100 a shekarar 2014. Kana, yankin da ke gabashin Asiya zai ci gaba da kasancewa wani yankin da ya fi samun bunkasuwa a duniya, an kiyasta cewa, tattalin arziki na yankin zai karu da kashi 6.1 cikin 100 a shekarar 2014 da ta 2015, cikinsu, tattalin arzikin Sin zai samu karuwa da kashi 7.5 cikin 100.(Bako)