in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban bankin duniya ya yabawa kasar Sin kan matakan da ta dauka na gyaran tattalin arziki
2013-12-11 10:54:14 cri
Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim ya bayyana cewa, matakan da da kasar Sin ta dauka na yi wa tattalin arzikinta gyare-gyare a kwanan baya sun karfafa zukatan masu ruwa da tsaki.

Jim Yong Kim ya bayyana hakan ne yayin wani karamin taron manema labaru da aka shirya a birnin Washington na kasar Amurka, ranar Talata 10 ga watan nan. Mr. Jim ya kara da cewa kwanan baya kasar Sin ta bayyana cewa, za ta sanya kasuwanni su taka muhimmiyar rawa wajen daidaita albarkatun kasar, kuma ta gabatar da matakan da suka hada da kafa yankin ciniki cikin 'yanci na Shanghai, da yin gyare-gyare game da tsarin shaidar mazauna yankunan kasar.

Har ila yau Sin ta dora muhimmanci sosai game da yunkurin aiwatar da gyare-gyare da ta tsara, kuma niyyarta ma ta ba wa al'umma kwarin gwiwa, kana saurin bunkasuwar tattalin arzikin ta daga watan Yuli zuwa watan Satumbar bana, lamari ne da ya zama wani abin albishir ga al'ummar ta.

Jim Yong Kim ya bayyana cewa, yanzu, tattalin arzikin duniya na fuskantar kalubale matuka, kuma manufar kudi da Amurka ta dauka ta haifar da babban tasiri ga kasashen duniya. Idan babban bankin Amurka ya daina gudanar da manufar sakin bakin aljihu yadda ya kamata, nan bada jimawa matakin zai haifar da karin lokaci ga kasashe masu tasowa wajen canja manufofinsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China