in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar share fage ta rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin ta farko ta isa kasar Mali
2013-12-05 11:36:41 cri

Kungiyar share fage ta rundunar sojan kasar Sin ta farko domin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali wadda take kunshe da sojoji 135 ta isa birnin Bamako, hedkwatar kasar a daren Laraba 4 ga wata, wadda kuma za ta gudanar da aikinta na kiyaye zaman lafiya a kasar na tsawon watanni 8.

Rahotanni na cewa, wannan ne karo na farko da kasar Sin ta tura rundunarta dake da karfin ba da tsaro, domin shiga aikin wanzar da zaman lafiya na MDD. Bayan isar rundunar a kasar Mali, za a girke dakarunta a birnin Gao karkashin jagorancin jihar yaki ta gabas na tawagar musamman ta MDD dake kasar Mali.

An ce za a dorawa wannan runduna aikin gyara hanyoyi, da gadoji, da hanyoyin filayen jiragen sama, da barikokin soja, da yin tsaron manyan sansanonin kwamandoji, tare da sauran ayyukan ceto.

A ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata ne dai kwamitin sulhu na MDD, ya zartas da kudurin kafa tawagar MDD domin kyautata halin da ake ciki a kasar Mali. Kuma bisa bukatar MDD, Sin ta yanke shawarar tura rundunar sojinta dake kunshe da sojoji 395 wadanda suka kasu sassa 3 wato sashen injiniyoyi, da rukunin sojin ba da jiyya, da rukunin masu ba da tsaro zuwa kasar ta Mali. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China