Sanarwar ta shugaba Conde ta zo bayan dawowarsa daga kasar Senegal kuma tana bisa tushen da matakan da shugabannin kasashen shiyyar yammacin Afrika suka dauka a yayin taronsu na ranar 25 ga watan Oktoba a birnin Dakar na kasar Senegal domin tattauna muhimman kalubalolin da shiyyar ke fuskanta a halin yanzu.
A cewarsa, batun tsaro na kowace kasa mambar kungiyar ECOWAS ya kamata ya kasance a tsakiyar manyan batutuwan domin yin hadin gwiwar ta yadda za'a fuskance su tare.
A yayin taron na shugabannin kasashen, mista Conde ya tabbatar da cewa ya tattauna tare da takwaransa na kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita kan sabuwar matsalar da kasarsa take fuskanta, musamman ma a yankin Kidal.
A cewar shugaba Conde, kasar Mali tana fama a yanzu da wani sabon yaki, inda kungiyoyin kishin islama suke wani yunkurin maida wannan yanki na kasar Mali a matsayin wani wurin da babu ikon gwamnatin kasar.
A cikin tsarin aikin tawagar kasa da kasa na tallafawa kasar Mali a karkashin tsarin Afrika ta MISMA, kasar Guinea tuni ta aika fiye da sojoji 150 a kasar Mali domin taimakawa kokarin da ake na yaki da ta'addanci a cikin wannan kasa dake yammacin Afrika. (Maman Ada)