in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 20 ne suka mutu a sakamakon nutsewar jirgin ruwa a Mali
2013-10-13 17:14:17 cri
Hukumar ba da kariya ga jama'ar kasar Mali ta bayyana a ranar 12 ga wata cewa, a daren ranar 11 ga wata, an yi hadarin nutsewar jirgin ruwa a yankin Mopti dake tsakiyar kasar Mali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 20.

Wani wanda abun ya faru gaban idonsa ya bayyana cewa, a daren ranar 11 ga wata da misalin karfe 11, wani jirgin ruwan dake dauke da mutane da kayayyaki da dama ya nutse a kogin Neja dake yankin Mopti. A lokacin kuma, mutane 250 zuwa 300 suna kan wannan jirgin ruwa. Wannan mutum ya kara da cewa, watakila jirgin ruwan ya nutse saboda yawan mutane da kayayyaki ya wuce yadda jirgin ruwan ya iya dauka, kawo yanzu ana ci gaba da aikin ceto.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China