A cikin wata hirarsa ta wayar tarho bayan hadarin, shugaban kasar Faransa Francois Holllande da takwaransa na kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita sun bayyana niyyarsu ta ci gaba yaki da kungiyoyin kishin islama dake arewacin kasar Mali.
A nasa bangare ministan harkokin wajen kasar Faransa ya yi alkawarin hada karfi da karfe tare da hukumomin kasar Mali domin gano dalilin mutuwar wadannan 'yan jarida. Shugaban diplomasiyyar kungiyar tarayyar Turai, Catherine Ashton ta bayyana bacin ranta matuka kan wannan kisan gilla tare jaddada goyon bayan kungiyarta ga kasar Mali game da kokarin da take na yaki da ta'adanci. Haka kuma a kasar Mali jam'iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hula a inuwar kawancen FDR domin yin allawadai da wannan kisa tare da yin kira ga hukumomin kasar su dauki matakan da suka wajaba kan matsalar ta'adanci. (Maman Ada)