in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai gawawwakin'yan jaridun Faransa su Biyu gida
2013-11-05 15:44:10 cri
Rahotannin baya-bayan nan na cewa, yanzu haka gawawwakin 'yan jaridun Biyu da suke aiki a gidan rediyon Faransa na RFI, Ghislaine Dupont, da Claude Verlon sun isa gida sakamakon harbe su da aka yi har lahira a kasar Mali da ke yankin yammacin Afrika.

Gwamnatin kasar Faransa ta bayyana a ranar 4 ga watan nan cewa, yanzu haka tana kokarin binciko wadanda ke da alhakin aikata wannan laifi na kisan 'yan jaridun. Haka kuma, jirgin saman da ya dauko gawawwakin 'yan jaridu su 2 ya tashi ne daga Mali zuwa Faransa, inda ya isa birnin Paris a ranar 5 ga wata Kana kuma shugaban kasar Faransa François Hollande ya kasance a filin jirgin sama domin tarbar gawawwakin.

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya ce, an riga an gudanar da bincike a wurin da lamarin ya auku, kuma ya zuwa yanzu, ba a tabbatar da ko su wane ne ke da alhakin aikata laifin ba, sai dai Fabius ya ce, Faransa za ta yi iyakacin kokarin cafke, tare da gurfanar da wanda ya aikata wannan ta'asa gaban kuliya.

A ranar 4 ga watan nan ne dai ma'aikatar tsaron kasar Faransa ta bayyana cewa, jim kadan da aukuwar lamarin, sojojin Faransa dake kasar Mali suka kara jibge sojoji a yankin Kidal, don tabbatar da tsaro a yankin. Yanzu haka dai yawan sojojin Faransa dake kasar ta Mali ya kai kimanin 3000.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China