Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ne ya bayyanawa manema labaru hakan a jiya Jimma'a. Haq ya ce burin Mr. Koenders na da burin ganin an kiyaye dukkanin dokokin da suka shafi zabe, tare da baiwa mata damar shiga a dama da su yayin zaben dake tafe.
Tuni dai rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDDr a Mali, ko MINUSMA, da hadin gwiwar hukumar UNDP, suka samar da tallafin kwararru da na kayan aiki da dama, domin tabbatar da nasarar zaben. Har ila yau ana sa ran baiwa hukumomin tsaron kasar tallafi na musamman, don ba da kariya ga wuraren zabe, musamman wurare dake da nisa da masu matsalar sufuri.
Tuni dai aka sanya ranar Lahadi 24 ga wata domin gudanar da zagayen farko na zaben 'yan majalissun kasar ta Mali, yayin da ake sa ran gudanar da zagaye na biyu a ranar 15 ga watan Disamba mai zuwa, duk dai a kokarin da ake yi na mai da kasar ta Mali, kan cikakkiyar turbar mulki karkashin tsarin mulkin kasar. (Saminu Alhassan)