Rahotanni daga yankin na Kidal sun ce, lamarin ya faru ne sakamakon kokarin da wasu masu zanga-zanga suka yi, na hana firaministan kasar shiga yankin na Kidal, wanda ke hannun 'yan tawayen azbinawa.
A cewar mai magana da yawun MDD Martin Nesirky, tawagar ta MINUSMA na fatan dukkanin sassan da wannan lamari ya shafa za su kai zuciya nesa, su kuma martaba yarjeniyoyin wanzar da zaman lafiya da aka kulla a baya.
Dauki ba dadin da sojojin gwamnati suka yi da masu zanga-zanga a Kidal din dai, ya sabbaba jikkatar mutane da yawa, ko da yake ba a tabbatar da yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba.
Mahukuntan kasar Mali dai na yunkurin farfado da yanayin zaman lafiya, da tabbatar da mulkin dimokaradiyya a kasar, bayan shafe shekaru ana dauki ba dadi da 'yan tawaye masu alaka da kungiyar Al-Qaida, wadanda suka kwace ikon yankin Arewacin kasar. Daga bisani aka kulla yarjejeniyar tsagaita wuta bayan tsoma bakin wasu kasashen duniya, da kwamitin tsaron MDD.(Saminu)