Bisa sanarwar da hukumar UNESCO ta bayar, an ce, za a fara aiwatar da shirin ne daga yankunan dake fama da yake-yake a arewacin kasar Mali, ciki har da Gao, Kidal, Timbuktu da kuma yankin Mopti dake gabas maso tsakiyar kasar. Abubuwan da ake bukatar kiyaye su sun hada da ilmin gargajiya, fasahohin hannu, adabi na baka, wake-waken tatsuniyoyi, bukukuwa da kuma wasu fasahohin gargajiya. Yayin da ake aiwatar da shirin a shekara ta biyu, za a maida hankali ga sauran yankunan kasar Mali. (Zainab)