Kakakin babbar hedkwatar ba da shawara ga rundunar Faransa Gilles Jaron, ya sanar a ran 24 ga wata da cewa, sojojin Faransa da na Mali, da kuma na MDD da yawansu ya kai kusa da 1500 sun dauki manyan matakan soji kan 'yan ga ni-kashe-ni a arewacin kasar Mali.
Gilles Jaron ya ce, makasudin daukar wannan mataki shi ne, dakile ayyukan 'yan ta'adda, tare da tabbatar da yanayin tsaro da ake ciki a kasar Mali. Ya ci gaba da cewa, matakin ba wai martani ne ga harin kunar bakin wake da wasu dakaru suka aiwatar a 'yan kwanakin baya ba.
Jaron ya ce kafin ranar 24 ga watan Nuwamba, gabanin kada kuri'ar zaben majalisar dokokin kasar ta Mali, dakarun sun himmatu wajen gudanar da ayyukansu. Hakan kuwa baya rasa nasaba da yiwuwar kaddamar da hare haren ta'addanci, da 'yan ga ni-kashe-ni dake sassan kasar ta Mali ka iya aiwatarwa a wasu muhimman lokuta.(Danladi)