Bisa shirin da aka yi, an ce, za a fara jefa kuri'a a ranar 24 ga wata da karfe 8 na safe, kuma za a kammala shi a ranar 18 ga wata. Bisa labarin da aka samu, an ce, masu zabe da yawansu ya kai sama da miliyan 6.5 ne za su kada kuri'u a zaben, kuma 'yan takara karkashin jam'iyyu da 'yan takara masu zaman kansu ne za su shiga zaben a gundumomi 55 na kasar.
Majalisar dokokin kasar Mali ita ce hukuma mafi girma ta kasar Mali, kuma 'yan majalisun da aka zaba, za su yi wa'adin tsawon shekaru 5. Za a gudanar da zagaye na biyu na zaben majalisar dokokin kasar a ranar 15 ga watan Disamba. (Bako)