in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta kara jibge sojoji a yankin arewa maso gabashin kasar Mali
2013-11-06 10:29:16 cri
A ranar 5 ga wata, yayin da ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ke zantawa da gidan rediyon kasar Faransa RFI, ya bayyana cewa, bayan da 'yan ta'adda sun yi garkuwa tare da kashe 'yan jaridun kasar sa guda 2 a ranar 2 ga wata a birnin Kidal dake kasar Mali, Faransa ta riga ta tura sojojin dake yankin kudancin kasar da yawansu ya kai 150 zuwa birnin Kidal, kuma sun hadu da sauran sojojin Faransa kimanin 200 dake wurin. A sa'i daya kuma, ya bayyana cewa, shawarar da shugaban kasar François Hollande ya yanke na kara tura sojoji a birnin Kidal ba zai canja ajandar janye jikin sojojin Faransa daga Mali ba.

Fabius ya bayyana cewa, kafin zaben majalisar dokoki na zagayen farko da za a yi a ranar 24 ga wata, Faransa za ta tabbatar da yawan sojojin da ta jibge a kasar. Daga bisani kuma, za ta rage yawan sojoji, a karshe dai ma, yawan sojojin kasar Faransa dake kasar Mali zai kai kimanin 1000, domin gudanar da aikin yaki da ta'addanci.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China