in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe shida masu shiga tsakani kan batun nukiliyar Iran sun cimma matsaya guda da kasar ta Iran
2013-09-29 21:00:30 cri

Wakilan kasashen shida masu shiga tsakani kan batun nukiliyar kasar Iran, sun yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar ta Iran a birnin New York hedkwatar MDD a yammacin jiya Alhamis 26 ga wata.

Wakilan kasashe 5 dake da kujeru din-din-din a kwamitin sulhu na MDD da suka hada da na kasar Sin, da Rasha, da Birtaniya, da Amurka da Faransa da kuma ministan harkokin wajen kasar Jamus, sun yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif. Bayan shawarwarin, kasashen Birtaniya, da Jamus da kungiyar tarayyar Turai ta EU suka shaida cewa, an yi su cikin yanayi mai kyau. Ko da yake dai sai cikin tsakiyar watan Oktoba mai zuwa ne ake sa ran gudanar da hakikkanin shawarwari kan wannan batu, a zaman da aka shirya gudanarwa a birnin Genewa na kasar Switzerland.

Da yake tsokaci kan wannan batu, Mr Mohammad Javad Zarif ya nuna cewa, an samu dan ci gaba a yayin shawarwarin kan yadda za a warware batun nukiliyar kasar Iran, a sa'i daya kuma, ya yi fatan za a janye takunkumin da aka garkamawa kasar ba tare da wani bata lokaci ba.

A sa'i daya kuma shugaban kasar ta Iran Hassan Rohani ya yi kira ga taron kwance damara na MDD da ya kafa wata yarjejeniyar hana amfani da makaman nukiliya daga dukkan fannoni, cikin jawabin da ya gabatar yayin taron da aka yi a wannan rana.

Da ma dai a baya ma yayin da shugaba Rohani ke zantawa da manema labarun kasar Amurka, ya taba bayyana fatansa na kaiwa ga cimma matsaya guda, tsakanin bangarori daban-daban da wannan batu na Nukiliya ya shafa cikin watanni uku zuwa shida.

Bugu da kari a dai wannan rana sakataren harkokin waje na kasar Amurka John Kerry, da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif, sun yi ganawa tsakaninsu, ganawar da ta kasance irin ta mafi girma tun shekaru 34 da suka wuce tsakanin jami'an kasashen biyu. Ana kuma sa ran cewa, za ta kasance wani mafari mai kyau wajen shawarwari na sabon zagaye kan batun nukiliyar kasar ta Iran. (Amina).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China