in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai bukatar kayyade lokacin gudanar shawarwari kan batun nukiliyar Iran, inji Faransa
2013-11-06 11:01:29 cri

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, da takwaransa na kasar Iran Mohammad Javad Zarif, sun yi musanyar ra'ayoyi kan sabon zagayen shawarwari tsakanin bangarori shida da kasar Iran, don gane da batun nukiliyar kasar, wanda za a yi daga ran 7 zuwa 8 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Manyan jami'an biyu sun gudanar da tattaunawar ne a jiya Talata 5 ga wata, a ofishin ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa.

Da yake tsomaci yayin ganawar tasu Fabius ya yi fatan samun ci gaba mai ma'ana yayin shawarwarin. Ya kuma nanata cewa kamata ya yi Iran, ta lura da damuwar da kasashen duniya ke nunawa, domin daukar hakikan matakin da ya dace, ta kuma amince a gudanar da bincike kan batun nukiliyarta, tare da kayyade lokacin gudanar da shawarwari. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China