A ran 21 ga wata ne, aka shiga rana ta biyu da kasashe shida da Iran suke yin shawarwari kan matsalar nukiliyar kasar ta Iran a birnin Geneva na kasar Switzerland. Bangarorin biyu sun tattauna kan cikakkun batutuwa na hakika, sai dai bambancin ra'ayoyi a tsakaninsu ya sanya ba a daddale kwarya-kwayar yarjejeniya, ta neman mafitar daidaita matsalar nukiliyar kasar ta Iran ba.
Da misalin karfe 9 na safiyar wannan rana, babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro, Madam Catherine Ashton, da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif, sun gudanar da tattaunawa a zagaye na farko na wannan rana. Bayan ganawarsu, Zarif ya bayyana cewa, akwai kyakkyawan fata game da shawarwarin da ya yi tare da Ashton, amma a sa'i daya akwai bambancin ra'ayi a tsakaninsu.
A kuma wannan rana da yamma, a yunkurin samar da ci gaba, Ashton da Zarif sun sake yin shawarwari, game da hakan, inda daga bisani kakakin Ashton, Mista Michael Mann ya bayyana shawarwarin da cewa, shawarwari ne masu amfani. Bayan haka, Madam Ashton ta sanar da shawarwarin da suka gudanar ga wakilan da suka zo daga kasashen nan shida masu ruwa da tsaki, domin su dauki matakan daidaita matsayin da ake ciki, an ce, kasashen shida sun tattauna tsakaninsu har cikin daren na jiya.
Ya zuwa yanzu, ba a kai ga samun daidaito tsakanin Iran da kasashen 6 ba, haka kuma su ma kasashen 6 ba su kai ga cimma matsaya ko ra'ayi guda ba. Don haka ake zaton za a ci gaba da kokarin rage bambancin ra'ayi da ke akwai a rana ta uku.(Danladi)