Yayin tattaunawar tasu, shugabannin biyu sun tabo irin nasarorin da suka cimma a hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, kana sun yi musayar ra'ayoyi kan kara bunkasa dankangantakar da ke tsakanin Sin da Malaysia daga dukkan fannoni karkashin yanayin da ake ciki.
Shugaba Xi ya ce, kasar Sin tana martaba dangantakar da ke tsakaninta da Malaysia, kuma dangantakar da ke tsakanin Sin da Malaysia tana kan gaba cikin dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN.
Bugu da kari shugabannin biyu sun tsara matakan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na shekaru biyar masu zuwa, kana sun amince kan cimma wani adadi na bunkasa dangankatar cinikayya tsakanin kasashen biyu na dala biliyan 160 ya zuwa shekarar 2017. (Ibrahim)