Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a tsibirin Bali na kasar Indonesiya a ran Litinin 7 ga wata, inda suka yi musayar ra'ayi kan wasu manyan batutuwa dake jawo hankalinsu da kuma dangantakar hadin kai ta sada zumunci.
A lokacin ganawar, Mr Xi ya nuna cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba mai armashi a wannan shekara. Sin da Rasha suna da moriya bai daya a yankin Asiya da Pacific don haka Sin na fatan kara hadin kai da kasar Rasha ta yadda za su kiyaye zaman lafiya da karko da kuma wadata a wannan yanki.
A nasa bangare, Mr Putin ya nuna cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na da makoma mai kyau, yana fatan cigaba da tuntubar juna tsakaninsa da shugaban kasar Sin. (Amina)