A yayin wannan ziyara tasa ta kwanaki biyu, mista Xi ya samu tattaunawa tare da shugabannin kasar Malaisiya, da yin musanyar ra'ayi bisa manyan batutuwan da suka shafi shiyoyi da kasa da kasa, da kuma shata makomar cigaban hulda tsakanin kasar Sin da Malaisiya.
Haka zalika shugabannin sun halarci bikin sanya hannu kan wasu jerin yarjeniyoyi na moriyar kasashen biyu.
Mista Xi da faraministan kasar Malaisiya Najib Razak sun dauki niyyar daukaka dangantakarsu bisa tushen huldar cin gajiya daga dukkan fannoni tare da kuma cimma yarjejeniya kan burin bunkasa yawan kasuwanci tsakanin kasashen biyu zuwa dalar Amurka biliyan 160 nan da shekarar 2017.
Jaridar kasar Malaisiya New Straits Times ya nuna a kan shafinta na farko a ranar Asabar cewa yarjejeniyoyin da aka cimma a yayin wannan ziyara ta Xi sun bude wani sabon babi na kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Kasar Malaisiya ita ce kasa ta biyu, ban da Indonesiya, a yankin Asiya dake Kudu maso gabas, da Mista Xi Jinping ya kai ziyara a wannan karo. (Maman Ada)