Shugaba Xi ya tashi daga birnin Jakarta zuwa na Kuala Lumpur bayan kammala ziyararsa a Indonesiya.
A yayin da yake ziyara a Malaysia, shugaba Xi zai gana tare da yin shawarwari da shugaban kasar, Abdul Halim Mu'adzam Shah, da firaministan kasar, Najib Razak, tare da halartar taron koli kan tattalin arziki.
A cikin 'yan shekarun da suka wuce, ci gaban dangantaka tsakanin Sin da Malaysia yana da kyau, kuma an sami ci gaba sosai wajen hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni daban daban.A bara jimillar kudin cinikayya tsakanin bangarorin biyu ta kai dala biliyan 94.8, har ma Sin ta kasance aminiyar Malaysia a fannin cinikayya mafi girma a duniya cikin shekaru hudu a jere, yayin da Malaysia ta zama aminiyar Sin a fannin cinikayya mafi girma a kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya cikin shekaru biyar a jere.
Malaysia ta kasance kasa ta biyu da shugaba Xi ya ziyarta a yankin kudu maso gabashin Asiya a wannan karo. Daga bisani kuma, shugaba Xi zai tashi zuwa tsibirin Bali na Indonesiya, domin halartar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 21 da za a yi a wurin.(Fatima)