in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Indonesiya
2013-10-03 17:01:31 cri
A ranar Alhamis 3 ga wata, a birnin Jakarta, fadar mulkin kasar Indonesiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Indonesiya Mista Marzuki Alie.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, shi da takwaransa na kasar Indonesiya Susilo Bambang Yudhoyono sun yanke shawarar inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu zuwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. Sin na fatan kara mu'amala da hadin gwiwa da Indonesiya a fannonin tattalin arziki, cinikayya, al'adu da sauransu.Akwai dankon zumunci tsakanin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar dokokin kasar Indonesiya. Ana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da karfafa muyasar fasahohi da koyo daga juna, ta yadda za a kara ba da gudummawa wajen inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Msita Marzuki a nasa bangaren ya yi maraba da zuwan shugaba Xi da yadda ya gabatar da jawabi a majalisar dokokin kasar Indonesiya. Ya ce, shugaba Xi ya kasance shugaban wata kasar waje na farko da ya yi jawabi a majalisar dokokin kasar, don haka majalisar tana marhabin da hakan. Kuma ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin Indonesiya da Sin na bunkasa lami lafiya. Hukumominsu na yanke shari'a suna mu'amala da juna sosai. Majalisar dokokin Indonesiya ta nuna goyon baya ga bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu, da fatan za ta karfafa mu'amala tsakaninta da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, a kokarin taka rawar a zo a gani wajen sa kaimi ga hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki, cinikayya, samar da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, tarbiyya da sauransu, da zummar ciyar da dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China