in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Indonesia da Sin sun amince su inganta dangantakar da ke tsakaninsu
2013-10-02 20:28:06 cri

A ranar Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Indonesia Susilo Bambang Yudhoyono, suka amince su inganta dangantakar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana yayin tattaunawar tasu cewa, kasashen biyu za su kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da daga darajar dangantakar zuwa wani sabon matsayi.

A jawabinsa shugaba Yudhonoyo na kasar Indonesia, ya ce kasashen biyu suna da aniyyar inganta dangantakar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare zuwa matsayin da ya dace.

Shugaban Xi jinping wanda ke ziyarar kwanaki biyu a kasar da ke yankin kudu maso gabashin Asiya,zai kuma halarci taron shugabannin kungiyar tattalin arziki ta kasashen yankin Asiya da Pacific karo na 21 da za a yi daga ranar 7 zuwa 8 ga watan Oktoba a wurin shakatawa na Bali da ke kasar Indonesia.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China