Shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya gana da alkalin kotun hukunta masu aikata manyan laifufuka ta duniya Sang-Hyun Song a jiya Talata 5 ga wata a Abuja fadar gwamnatin kasar, inda ya nuna cewa, Nijeriya ba za ta janye jikinta daga kotun ba, amma za ta hada kai da kungiyar tarrayar Afirka AU, MDD da dai sauran kasashe mambobin kotun, domin sake nazarin ka'idojin da kotun ta dauka, da kuma sa kaimi ga kwaskwarima kan wannan kungiya.
Ya ce ya kamata, kotun ta mai da hankali kan halin da ake ciki tare kuma da fahimtar halin da shugabannin kasashen Afrika suke ciki da damuwar da suke nunawa. (Amina)