in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin kula da hakkin Bil-Adama na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar a Nijeriya
2013-11-06 14:36:37 cri

Mai magana da yawun ofishin babban kwamishinan kula da hakkin Bil-Adama na MDD, Madam Cecile Pouilly, ta yi Allah wadai da harin da aka kai jihar Borno, dake arewa maso Gabashin tarayyar Najeriya a ranar 5 ga wata, tana mai bayyana harin, wanda ake zaton 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne suka gudanar da shi, a matsayin tsantsar rashin tausayi.

Madam Pouilly ta kuma yi kira ga mahukuntan kasar, da su tabbatar jami'an rundunar soji, na bin doka da oda yadda ya kamata, yayin da suke aiwatar da aikinsu, domin kaucewa nuna karfin tuwo kan fararen hula.

Ana dai zargin magoya bayan kungiyar ta Boko Haram da kai wannan hari ne, kan jerin gwanon wasu motoci dauke da 'yan bikin Aure, dake kan hanyarsu zuwa jihar Borno, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 30, ciki hadda wasu sojojin hudu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China