Bisa kididdigar da hukumar UNHCR ta bayar, an ce, yake-yaken da aka yi a yankin arewa maso gabashin kasar Nijeriya sun haddasa mutuwar mutane a kalla 5000. Hukumar UNHCR ta ce, sabo da yadda lamarin yaki-ci-yaki-cinyewa, ya sa an kasa gudanar da aikin jin kai da bincike a wurin, sakamakon haka yawan 'yan gudun hijira zai iya karuwa. Hukumar UNHCR ta yi kira ga kasashen dake makwabtaka da Nijeriya da su bude kan iyakokinsu, ta yadda, za a samar da gudummawar kasa da kasa ga 'yan gudun hijira na kasar Nijeriya da suka arce don gujewa yake-yake.
Kakakin hukumar UNHCR Dan McNorton ya bayyana cewa, kwanan baya, hukumar ta bayar da wata sanarwa, da muradin taimakawa aikin jin kai ga 'yan gudun hijira na Nijeriya. Ya bayyana cewa, kafin yanayin tsaro da ake ciki da hakkin kare dan Adam a yankin arewa maso gabashin Nijeriya ya samu kyautatuwa, ko 'yan gudun hijira za su koma gidajensu lami lafiya, za a ci gaba da aiwatar da wannan sanarwa.(Bako)