131028murtala
|
Gwamnatin jihar Borno dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya za ta sake gina wasu gidaje dari biyu, wadanda aka rusa a yankin Kawuri na karamar hukumar Konduga a satin da ya gabata, sakamakon wani harin da 'yan bindiga suka kai yankin.
Mataimakin gwamnan jihar, Zannah Mustapha ne ya fadi hakan a lokacin da ya ziyarci kauyen da lamarin ya shafa, inda ya ce, gwamnati zata taimakawa 'yan kasuwar da suka rasa shagunansu sakamakon farmakin da aka kai musu.
Zannah Mustapha ya kuma bukaci shugaban rikon karamar hukumar Konduga da ya lissafa adadin gidajen da gwamnati zata ba su wannan taimako na gaggawa.
Bisa labarin da muka samu daga kamfanin dillancin labarai na kasar Najeriya wato NAN, an ce, sama da mutane 18 ne harin ya rutsa da su a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan kauyen da yayi sanadiyyar rushewar gidaje dari biyu, da shaguna 50, tare kuma da motoci masu tarin yawa.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.