in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kotun Nijeriya ta yi watsi da tuhumar da aka yiwa wasu 'yan Rasha
2013-10-09 16:43:24 cri
A ranar 8 ga wata, wata babbar kotun tarayya da ke birnin Lagos, cibiyar cinikayyar tarayyar Najeriya, ta yi watsi da tuhumar aikata laifin fasa-kwaurin makamai, da aka yiwa wasu ma'aikatan jirgin ruwa 'yan asalin kasar Rasha su bakwai.

Wannan hukunci dai ya kawo karshen halin rashin tabbas da dangantakar Nijeriya da Rasha ta shiga a tsawon shekara guda.

A watan Oktobar bara ne dai sojojin ruwan Nijeriya sun cafke wani jirgin ruwan kasar Rasha, mai dauke da makamai iri-iri, da dubban albarusai a yankin tekun Guinea da ke kusa da jihar Lagos, wadanda suka ce anyi safarar su ba bisa ka'ida ba. Har ila yau sojojin Najeriyar sun tsare ma'aikatan jirgin ruwa su 15, sannan a watan Janairun bana, gwamnatin tarayyar kasar ta yanke shawarar gurfanar da su gaban kotu, bisa zargin fasa kwaurin makamai.

Daukar wannan mataki ya sanya ma'aikatar kula da harkokin wajen Rasha ta rika bukatar Nijeriya ta saki ma'aikatan jirgin ruwan. A kuma watan Yunin bana, wata kotun Nijeriya ta sanar da yin watsi da tuhumar da aka yiwa 'yan Rasha 8 daga cikin 15 da aka cafke.

Sa'an nan a ranar 8 ga wata, wata kotun tarayya dake birnin Lagos, ta sanar da yin watsi da tuhumar da aka yi wa sauran'yan Rasha su 7, tare da bada umarnin sakinsu, matakin da ya kawo karshen wannan batu baki daya. Sai dai yayin da ake gudanar da shari'ar, ma'aikatan jirgin ruwa su 7, ba su fayyace hujjar ajiye wadannan makamai cikin jirgin ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China