in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fama da cutar Kwalara a wasu sassan Najeriya
2013-10-24 15:40:31 cri

A halin yanzu, cutar kwalara na ci gaba da addabar wasu jihohin tarayyar Najeriya, lamarin da ke ci wa jama'a tuwo a kwarya. Jihohin da aka samu barkewar cutar sun hada da Lagos, da Plateau, Zamfara da sauransu.

A 'yan kwanan baya bayan nan an samu barkewar cutar kwalera mai tsanani a wasu kananan hukumomi akalla biyar dake jihar Lagos, ciki har da Ajeromi, da Apapa, da tsibirin Lagos, da Oshodi-Isolo da Surulere. Rahotanni sun kuma nuna cewa, akalla mutane uku sun rasa rayukansu, baya ga wasu da dama dake jinya a asibiti.

Kwamishinan ma'aikatar kiwon lafiyar jihar ta Lagos Dr. Jide Idris ya tabbatar da hakan a Ikeja dake birnin Ikko, inda ya bukaci jama'a da su ziyarci asibitin dake kusa da su ba tare da bata lokaci ba, da zarar sun ga alamun kamuwa da wannan cuta.

Dr. Jide Idris ya kuma bayyana cewa, gurbataccen abinci da ruwan sha a wasu kananan hukumomi ne babban dalilin da ya jawo barkewar cutar ta kwalara a jihar.

Har wa yau kuma, kwanaki uku kafin barkewar cutar a Lagos, rahotanni daga jihar Plateau dake tsakiyar Najeriya sun ce, mutane akalla 8 sun mutu sakamakon cutar ta kwalara.

A jihar Zamfara ma, mutane da dama na fama da wannan cuta, inda da daman su ke karbar magani a asibiti.

Rahotannin sun kuma jaddada cewa, rashin tsabtataccen muhalli, da rashin bin hanyoyin da suka dace wajen kiwon lafiya, tare kuma da shan gurbataccen ruwa su ne ummul aba'isin barkewar cutar ta kwalara. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China