Kungiyar kare hakkin 'dan Adam ta duniya Amnesty International, wadda hedkwatarta ke birnin London, ta gabatar da wani rahoto a ran 16 ga wata cewa, tun lokacin da aka ayyana dokar ta baci don yaki da ayyukan ta'addanci a arewa maso gabashin Niejriya ya zuwa yanzu, fararen hula da yawansu ya kai kusan dubu ne suka mutu.
A cikin wani rahoton da kungiyar Amnesty International ta gabatar, ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta gudanar da bincike mai zaman kansa game da wadannan abubuwa da suka faru a jere, domin kawo karshen take hakkin 'dan Adam. Amma gwamnatin Nijeriya ba ta ba mayar da wani martani ba.
Ana bukatar samun karin shaidu domin babbatar da rahoton da kungiyar Amnesty International ta gabatar. Kafin haka, wasu kamfanonin dillancin labaru na yammacin duniya sun watsa labarai cewa, sojojin Nijeriya sun kama mutame fiye da dari a wani samamen da suka kaddamar a watanb Agusta, har zuwa yanzu yawancin mutanen da ake tsare da su ba a sake su ba. Sabo da haka kungiyar Amnesty International tana ganin cewa, an riga an kashe wadannan mutane, abin da kungiyar ta tunanin cewa sojojin na Nijeriya sun keta hakkin 'dan Adam. Amma idan kungiyar ba ta da cikakkun shaidu, ba za a iya amincewa da rahotonta ba.(Danladi)