Kakakin rundunar 'yan sanda Emeka Chukwuemeka na jihar ya bayyana cewa, lamarin ya faru a wani wurin addu'a na wannan coci a yankin Uke da ke arewacin jihar. Kuma bisa labaran da kamfanonin dillacin labarai na wurin suka bayar, an ce, kimanin mutane 30 sun rasu, amma Mr. Chukwuemeka ya ce, ba a iya tabbatar da yawan mutane da suka rasu cikin wannan hadari ba, sabo da wasu mutane sun farka bayan da suka suma.
A halin yanzu, 'yan sanda suna bincike kan wannan lamari. (Maryam Yang)