131031murtala.m4a
|
Shahararriyar mujallar harkokin kasuwancin nan ta kasar Amurka mai suna Forbes ta bayyana jerin sunayen mutane masu karfin fada-a-ji a duniya a shekara ta 2013, inda shugaban gamayyar kamfanin nan na Dangote a tarayyar Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya ke matsayi na 64, abun da ya sa ya zama mutumin da ya fi kowa karfin fada-a-ji a Afirka.
Dangote mai shekaru 56 shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka baki daya, sa'annan ya fi duk wani bakar fata a fadin duniya, haka kuma shi ne dan Afirka daya tilo a cikin mutane 70 mafi karfin fada-a-ji a duniya a wannan karo, sai kuma dan kasar Sudan, Mo Ibrahim da yake biye masa baya.
A cikin jerin masu karfin fada-a-ji a duniya guda dari na wannan shekara, babu wani shugaban kasa daga Afirka ko guda daya.
Bisa sunayen mutanen da mujallar Forbes ta fitar, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ne ya fi kowa karfin fada-a-ji a duniya, yayin da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama ke biye masa baya, sai kuma shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya ke matsayi na uku.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.