in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya da Isra'ila sun daddale yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama a tsakaninsu
2013-10-29 10:24:39 cri
A ranar Litinin 28 ga wata a birnin Kudus, Nijeriya da Isra'ila suka daddale yarjejeniya game da zirga-zirgar jiragen sama a tsakaninsu, wadda ta taimaka wajen bude hanyar zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye a tsakaninsu. A madadin shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan, mataimakiyar ministan harkokin waje na kasar Nijeriya Viola Onwuliri ta sa hannu kan yarjejeniyar tare da bangaren Isra'ila.

Kafin wannan, idan 'yan kasar Nijeriya ciki har da Kiristoci masu ziyarar Ibada suna son zuwa kasar Isra'ila, tilas su canja jiragen sama a kasashen dake makwabtaka da Isra'ila. Bayan da aka daddale wannan yarjejeniya, bisa ka'idar samun moriyar juna, ana saran kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da kasashen biyu suka baiwa izni za su iya fara jigila kai tsaye a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China