Shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya sanar a safiyar Litinin 7 ga wata da cewa, ya kafa wani kwamitin ba da shawara mai kunshe da mutane 13, da zummar share fagen babban taron kasar wanda zai warware matsalolin da kasar ke fuskanta da tabbatar da makomar kasar.
A gun bikin kafuwar kwamitin da aka yi a Abuja babban birnin kasar. Shugaba Jonathan ya bayyana cewa, manyan ayyuka dake gaban kwamitin na da muhimmanci sosai, a cewarsa babban taro zai wakilci daukacin jama'ar kasar, don haka ya kamata a kiyaye moriyar jama'a yayin da ake shirya tsarin taron.
An ce, shugaban ya baiwa kwamitin makonni shida wajen gudanar da aikin share fage.
Shugaba Jonathan ya gabatar da wannan shiri ne lokacin da yake jawabi a ranar 1 ga watan Oktoba don taya murnar cika shekaru 53 da samun 'yancin kan kasar.
Femi Okurounmu shi ne zai shugabanci kwamitin, yayin da Akilu Indabawa ya zama babban sakatare. (Amina)