Ba safai a kan iya samun husufin rana irin na wannan karo ba, kuma wuraren da aka iya kallon cikakken husufin rana sun hada da kasashen dake kusa da tsakiyar duniya wato Equator kamar su kasashen Gabon, Kongo(Brazzaville), Kongo(Kinshasa), Uganda, Kenya, Habasha, da Somaliya.
An samu wannan husufin rana a ranar 3 ga wata da karfe 1 da minti 13 zuwa karfe 3 da minti 27 da yamma bisa agogon GMT, inda kuma, za a samu cikakken husufin rana da karfe 2 da minti 25 na yamma, kuma wannan cikakken husufin rana zai dade har minti 1 da dakika 39.(Bako)