Binciken cibiyar Afrobarometer ya nuna cewa talaucin da ake fuskanta yana nan ko'ina a nahiyar Afrika, da karyata wasu alkaluman hasashe dake nuna cewa ja da bayan talauci zai biyo cigaban adadin bunkasuwar GDP na kasashen.
Cibiyar Afrobarometer wani tsari ne na bincike mai zaman kansa da ba ya da wata alaka da kowa dake auna yanayin cigaban jama'a, siyasa da tattalin arziki a nahiyar Afrika.
Wannan bincike ya tattara alkaluma a cikin kasashen Afrika 34 tsakanin watan Oktoban shekarar 2011 da kuma watan Yunin shekarar 2013, bisa wani babban shirin dake la'akari da ra'ayi da kuma darusan zaman rayuwar mutane. A cikin kasashe 16 inda aka aza tambayoyi a tsawon shekaru talatin da suka gabata, an samu 'yan alamu na ragowar talauci da ake fama da shi duk da alkaluman cigaban GDP da kashi 4.8 cikin 100 a kowace shekara bisa mizalin da ake samu bisa wannan lokaci a cewar masanan Afrobarometer a cikin rahotonsu.
Ana ganin sosai ja da bayan talauci a cikin kasashe biyar kamarsu Cap-Vert, Ghana, Malawi, Zambiya da Zimababwe, amma ana ganin karuwar talauci a cikin kasashe biyar da suka hada da Botswana, Mali, Senegal, Afrika ta Kudu da Tanzaniya in ji wannan rahoto. (Maman Ada)