A cikin wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu Mac Maharaj ya bayar, an ce, ko da yake wani sa'i Nelson Mandela bai samu daidaituwa ba wajen ciwonsa, amma likitocin sun ce, tsohon shugaban kasar ya nuna babban karfin samun farfadowa, sabo da haka halin da yake ciki wajen ciwonsa ya fara daidaituwa bayan da aka ba shi magani.
A cikin sanarwar da Magaraj ya bayar, an ce, likitoci na kokarta kawo sauki ga jikin Mandela. A sa'i daya kuma, shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacon Zuma ya yi kira ga al'ummar kasar da su ci gaba da yin addu'o'i ga Mandela.
Wannan shi ne karo na farko da fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu ta bayar da sanarwa game da halin da Mandela ke ciki cikin makwanni biyu da suka gabata. Tuni dai a farkon wannan wata, fadar shugaban kasar Afrika ta kudu ta ba da sanarwa cewa, jikin Mandela ya samu sauki, amma ya zuwa yanzu, halin da yake ciki ya yi tsanani.(Bako)