Rahoton ya bayyana cewa, mutane 70 ne kawai suka mutu a kasar a shekarar bara sakamakon cutar Malaria, yayin da a shekarar 2000, wannan adadi ya kai 460. A yankunan da aka fi samun cutar, yanzu, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya ragu zuwa kasa da kashi 0.1 cikin 100.
Ministan kiwon lafiya na kasar Afrika ta Kudu Aaron Motsoaledi ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta yi shirin kawar da cutar Malaria zuwa shekarar 2018. Matakan da kasar ta dauka wajen cimma wannan buri sun hada da kashe sauro dake yada cutar, kyautatuwar yanayin kiwon lafiya na jama'a, kara fadakar da jama'a, da yin kokarin samar da jinya ga wadanda suka kamu da cutar.(Bako)