Wannan rahoto ya bayyana cewa, sakamakon kammala tsarin nuna bambancin launin fata a kasar Afrika ta Kudu cikin shekaru 20 da suka gabata ya sa, tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba cikin hanzari, kuma yawan tattalin arziki da aka samu ya ninka sau 2. Amma wannan rahoto ya ci gaba da nuna cewa, tattalin arzikin kasar na ci gaba da fuskantar kalubaloli da dama. Yanzu, yawan mutanen da suka rasa guraben aikin yi ya zarce kashi 24 cikin 100, cikinsu, akasarinsu matasa ne. A sa'i daya kuma, akwai babban gibin a tsakanin masu kudi da talakawa, kuma kashi 85 cikin 100 na bakaken fata na kasar, albashinsu kalilan ne, yayin da kasha 87 cikin 100 na fararen fata, albashinsu ya ked a yawa.
Haka kuma, wannan ra'ayi ya dace da ra'ayin gwamnatin kasar Afrika ta Kudu. A watan Oktoba na bana, shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, yanzu,matsakaicin albashi na ko wane gida na fararen fata ya ninka sau 6 da takwarorinsu na bakaken fata, kuma al'ummar kasar na fuskantar talauci da rashin samun daidaito, da rashin samun guraben aikin yi, sannan da rashin samun fahimta.(Bako)