Sanarwar ta ce, bala'in girgizar kasar ya kuma raunata mutane 4152, tare da lalata gine-gine dubu 6. Har zuwa yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto yadda ya kamata.
A baya a ranar 28 ga wata, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Jiang Yu ta ce, gwamnatin Sin ta kuduri aniyar samar da tallafin tsabar kudi dala miliyan 1 ga gwamnatin Turkiyya. Ta ce, a baya kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta bada kudi dala dubu 50 kyauta ga kungiyar agaji ta Red Crescent, kuma Sin na son ci gaba da samar da tallafi ga kasar Turkiyya in bukatar hakan ta taso.
Har wa yau kuma, a ranar 28 ga wata, hukumar kula da harkokin 'yan gudun-hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta sanar da cewa, za ta yi jigilar kayayyakin ceto ta sama zuwa yankin gabashin Turkiyya da bala'in ya ritsa da shi, ciki har da tantuna dubu 4, barguna dubu 50, gami da kananan tantunan tafi-da-gidanka dubu 10.(Murtala)