Ban da wannan kuma, wannan bala'in ya yi sanadiyyar abkawar gine-gine har 2200 yayin da mutane kusan 1300 suka raunana.
A game da wannan lamari, ya zuwa yanzu shugabannin kasashe ko yankuna 51 sun bugawa shugabanni da gwamnatin kasar Turkiya waya domin jajenta masu.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, kasar Turkiyan ta riga ta tura motocin agaji 450 domin aikin ceto . Kuma ya zuwa yanzu an riga an daidaita batun samar da kayayyaki da abinci da ruwan sha da ake bukata cikin gaggawa a yawancin yankunan da bala'in girgizar kasar ya shafa.(Amina)