Bala'in tsunami zai isa yankunan gabashin Afirka dake bakin tekun Indiya
Bisa bayanin da tashar yin hasashen yanayin teku ta kasar Sin ta fitar a ranar Laraba 11 ga wata, an yi hasashen cewa, bala'in tsunami da aka haifar da shi sakamakon bala'in girgizar kasa da aka samu a yankunan teku dake kusa da tsibirin Sumatra na kasar Indonesiyya a wannan rana da yamma zai isa yankunan kasashen Indiya da Sri Lanka bayan sa'o'i biyu da aukuwar bala'in girgizar kasar, sannan zai isa yankunan tsibirin Larabawa da gabashin Afirka da na arewa maso yammacin Australiya wadanda suke bakin tekun Indiya bayan sa'o'i biyar da wannan bala'in girgizar kasa. (Sanusi Chen)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku