Bisa bayanin da hukumar binciken labarin kasa ta kasar Amurka ta samu, an ce, wannan bala'in girgiza kasa ya faru a yankin tekun dake nesa da birnin Banda Aceh, hedkwatar lardin Aceh da kilomita 431, kuma zurfin wannan bala'in dake karkashin kasa ya kai kilomita 33.
Cibiyar yin gargadin aukuwar bala'in tsunami ta tekun Pasifik ta ce, gargadin yiyuwar aukuwar bala'in tsunami a tekun Indiya ya riga ya fara aiki. An yi hasashen cewa, tsunami na farko zai kai bakin teku na lardin Sumatra da misalin karfe 6 da minti 21 na ranar 11 ga wata da maraice bisa agogon Beijing.
An taba gamuwa da bala'in tsunami mai tsanani sosai a lardin Aceh a karshen shekarar 2004, inda ya yi sanadiyyar mutuwa da bacewar mutane dubu 170 a kasar Indonesiyya, tare da mutane kimanin dubu 230 da suka mutu a sauran kasashe 13 dake bakin tekun Indiya. (Sanusi Chen)