Shafin Internet na Afrika ta Kudu ya ba da labari cewa, bayan aukuwar girgizar kasa, kungiyar ceton mutane ta kasar Sin ta je yankunan da bala'in ya ritsa da su ba tare da bata lokaci ba don ceton mutane. Bisa labarin da aka bayar, an ce, sabo da wahalar tafiya zuwa wurin, an gamu da cikas wajen ceton mutane, sabili da haka, jama'a da dama suna bukatar ruwan sha da tantuna a wuraren da bala'in ya shafa.
Su ma, jama'ar kasar Nijeriya sun nuna damuwa sosai game da bala'in girgizar kasa, inda suka aika da wasikun jaje ga wakilin gidan rediyon CRI da ke Nijeriya, don nuna tausayi ga jama'ar kasar Sin. Daya daga cikinsu Hajiya Suwaiba Suleiman dake aiki a gidan rediyon Aso dake birnin Abuja hedkwatar tarayar Nijeriya wadda ke da wasu labaru na kasar Sin sosai. Ta sanar da wakilinmu cewa, abin da ya burge ta game da kokarin ba da ceton shi ne, yadda bayan aukuwar girgizar kasa, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya je yankunan da girgizar kasa ta shafa da kanshi ba tare da bata lokaci ba. Ta ce, da isar Mr. Li wannan wuri ya sa hannu wajen aikin ceto. Ganinta, wannan ya nuna cewa, shugabannin kasar Sin sun san yadda za su yi a ayyukansu don moriyar jama'a da dukuyoyin mutane ba tare da ba da kaskanci ga jama'arsu ba, wannan abin koyi ne sosai.(Bako)