Bisa labarin da kafar yada labaru ta kasar ta bayar, an ce, gine-gine da dama sun abka sakamakon bala'in, lamarin da ya jawo mutane da dama suke binne a karkashin buraguzan gine-ginen, hakan yasa ake kiyasin cewa, yawan mutanen da suka mutu zai wuce adadin da ake tsammani.
Bisa labarin da kafar yada labaru ta kasar Iran ta bayar, an ce, girgizar kasar ta haddasa asarar wasu gine-gine a birnin Chaldran na kasar Iran dake kan iyakar kasashen biyu kuma ya katse layin sadarwa na yanar gizon Intanet a wurin.
A dangane da wannan a ranar lahadin nan 23 ga wata, jami'in kungiyar IFRC Mahmoud Mozaffar ya bayyana cewa, Iran tana shirin turawa kasar Turkiya rukunin ceto.
A wannan rana kuma, ministan tsaron Isra'ila Ehud Barak ya ce, kasar tana fatan baiwa kasar Turkiya dukkan tallafi gwagwadon karfinta.(Amina)