in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kawo karshen harin da wasu 'yan bindiga suka kai a wata cibiyar kasuwanci dake kasar Kenya
2013-09-25 09:20:27 cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi wani jawabi ta gidan telebijin mallakar kasar a daren jiya Talata, inda ya bayyana cewa yanzu haka sojojin kasar sun cimma nasarar dakile ayyukan da 'yan ta'adda suka yi na yin garkuwa da mutane, a wata babbar cibiyar kasuwanci mai sunan Westgate dake Nairobi babban birnin kasar ta Kenya.

Cikin jawabin nasa, shugaba Kenyatta ya furta cewa,bayan fafatawar da aka yi tsakanin 'yan ta'adda da sojojin kasar Kenya, an kai ga dakile ayyukan maharani dake tsare da mutane har tsawon kwanaki hudu. Ya zuwa yanzu wannan harin ta'addanci ya yi sanadin mutuwar mutane tare da jikkata da yawansu ya kai 240.

Shugaban kasar ta Kenya ya kara da cewa, cikin mutanen da aka hallaka akwai fararen hula 61, da sojojin kasar 6, an kuma harbe 'yan ta'adda 5. Dadin dadawa, an kama wasu mutum 11, wadanda aka tuhuma da hannu cikin aukuwar lamarin.

Kenyatta ya kuma cewa, mai yiwuwa ne akwai 'yar Birtaniya 1, 'yan kasar Amurka 3 ko 4, cikin wadanda ake zargi da shirya kai harin. Ya zuwa yanzu, an rufe cibiyar kasuwancin da wannan lamari ya auku, sannan masu aikin ceto na ci gaba da tantance gawawwakin wadanda suka rasu, kafin tabbatar da hakikanin yawan wadanda suka mutu.

Ban da haka, Uhuru Kenyatta ya sanar da cewa, daga ran 25 ga wata, za a sauke tutar kasar zuwa rabin sanda, da yin zaman makokin kwanaki uku a dukkanin fadin kasar domin nuna alhini ga wadanda aka rasa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China