Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da firaministan kasar Birtaniya David Cameron sun nuna a ran 22 ga wata a birnin Paris cewa, kasashen biyu za su nemi EU da ta soke takunkumi da ta sanyawa 'yan adawa a kasar Sham na hana sufurin makamai a taron ministocin harkokin waje na EU da za a yi a ran 27 ga wata.
Francois Hollande ya ce, yanzu, halin da ake ciki a wasu wurare dake kasar Sham ya yi amfani ga gwamnatin kasar Sham, saboda gwamnati na da makamai, amma 'yan adawa babu. Ya jaddada cewa, za a cimma wani tsarin daidaita rikicin kasar Sham a gun taron kasa da kasa kan rikicin kasar Sham da za a yi a watan Yuni a birnin Geneva na kasar Switzerland, kasashen Faransa da Birtaniya za su matsin lamba kan wannan aiki.
A wannan rana kuma, ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov ya gana da mataimakin firaministan kasar Sham Fayssal Mikdad a birnin Mascow, inda ya nuna cewa, ya kamata, bangarori daban-daban da abin ya shafa su tabbatar da daina bude wuta da yi shawarari tsakaninsu tun da wuri.
Sergei Lavrov ya ce, Rasha da Amurka sun yi kira da a gudanar da wannan taro da zummar fatan jama'ar kasar Sham da kansu su zabi hanyar bunkasuwar kasa nan gaba ba tare da samu tsoma baki daga sauran kasashe ba. Ban da haka, ya darajanta matsayin da gwamnatin kasar Sham ta yi na karbi wannan shawara, kuma yana fatan 'yan adawa sun amince da wannan shawara.
Fayssal Mikdad kuwa a nashi bangare, ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sham na fatan a dakatar harba makamai a kasar nan take. Ya kuma nanata cewa, gwamnati na shirya yin shawarwari da 'yan adawa. Game da batun ko kasar Sham za ta shiga taron kasa da kasa kan rikicin kasar Sham ko a'a, Fayssal Mikdad yana mai cewa, gwamnatin na nazari kan wannan batu, kuma za ta yanke shawara cikin gajeren lokaci. (Amina)